Kungiyoyin Palastinu na gudanar da taro a Masar
Kungiyoyin Palastinu na gudanar da taro a Masar da nufin magance matsalar rayuwa ta Al'ummar yankin zirin Gaza
Kamfanin dillancin labaran Xin huwa na kasar China ya habarta cewa a jiya Laraba ne kungiyoyin Palastinawa suka tattaunawa kan matsalar da Al'ummar zirin gaza ke fuskanta kama daga matsalar karamcin abinci, kuncin rayuwa da kuma yadda za a sake gina gidaje da kuma cibiyoyin da Haramcecciyar kasar Isra'ila ta rusa a harin wuce gona da irin da ta kaiwa yankin a shekara 2014, a garin Ainun Sahana dake gabashin kasar Masar.
A yayin taron wakilan Palastinawan sun bukaci Gwamnatin Masar da ta bayar da izini na shigar da kayan gine-gine zuwa yankin zirin Gaza.tare kuma da kiran dukkanin bangarorin siyasa gami da na fararen hular Palastinu na suka gudanar da taron kasa a birnin Alkahira.
Shi dai wannan taro na a matsayin taron zartar da yarjejjeniyar da kungiyoyin Palastiwan suka cimma a birnin Alkahira tare kuma da kokari wajen dinge barakar dake tsakanin su.
Tun bayan da kasar Masar ta rufe hanyar Rafah, Al'ummar zirin Gaza mai mutane milyan daya da dubu 900 suka shiga cikin mayuwacin hali na karamcin abinci da kuma matsalar tattalin arziki.