Burundi: Yan sandan Sun kame Wasu 'yan Jarida biyu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13768-burundi_yan_sandan_sun_kame_wasu_'yan_jarida_biyu
Yansanda sun kame yan jarida Biyu
(last modified 2018-08-22T06:59:13+00:00 )
Nov 12, 2016 08:38 UTC
  • Burundi:  Yan sandan Sun kame  Wasu 'yan Jarida biyu

Yansanda sun kame yan jarida Biyu

Radiyon Faransa na kasa da kasa ya ambato majiyar 'yan sandan kasar Burundi na cewa; an kame wasu fitattun 'ya jarida biyu a jiya juma'a.

Majiyar ta ci gaba a cewa wadanda aka kame din sun hada da Leon Masengo da shi ne edita mai kula da shafukan intenret na Radiyon Bonesha FM, sai kuma wani mai karanta labaru a Rediyon.

Radiyo Bonesha FM dai ya bayyana wani jami'in yan sanda mai suna Desire Uwamahoro da hannu a murkushe al'ummar kasar bayan tazarcen shugaba Pierre Nkurunziza.

Sharhi da labarun da Rediyon ya  watsa, ya biyo baya kame dan sandan ne da zargin hannu a cikin fasakwaurin zinariya.