Masar : Morsi Da Badie Sun Tsira Daga Hukuncin Kisa
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i13933-masar_morsi_da_badie_sun_tsira_daga_hukuncin_kisa
Kotun karya shari'a a Masar ta yi watsi da hukuncin kisa da aka yankewa hambararen shugaban kasar Muhammad Morsi dama jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi Mohamed Badie.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Nov 15, 2016 13:41 UTC
  • Masar : Morsi Da Badie Sun Tsira Daga Hukuncin Kisa

Kotun karya shari'a a Masar ta yi watsi da hukuncin kisa da aka yankewa hambararen shugaban kasar Muhammad Morsi dama jagoran kungiyar 'yan uwa musulmi Mohamed Badie.

Ko bayan ga wadanan mutanen biyu kotun ta kuma dakatar da hukuncin da aka yankewa wasu jigan-jigan kungiyar ta 'yan uwa musulmi.

Bayan wannan matakin kotun yanzu dai za'a sake gabatar da mutanen gaban wata kotu domin su fuskanci shari'a, saidai fa koda tsohon shugaban ya tsira daga hukuncin kisan ba zai kubuta ba daga hukuncin shekaru 20 da kotun karya shari'ar ta tabbatar a gare shi.

A watan Yuni shekara 2015 data gabata ne wata kotun kasar ta yanke hukuncin kisa ga tsohon shugaban kasar bisa haraka nan ta tserewar wasu fursuna a wani gidan kurkuku na kasar.

Ko baya ga hakan kotun ta tuhumi Mista Morsi da Badie da kuma wani jigo a kungiyar ta 'yan musulmi da kisan wasu mutane goma a wani hari da aka kai a gidan kurkukun Wadi al-Natroun a farkon borin kin jinin gwamnatin Hosni Mubarak a watan Janairu na shekara 2011.