Gargadin Unicef Akan Yaran Afirka Ta Tsakiya
Yaran Afirka ta tsakiya suna fama da matsala a zaman gudun hijira
Kamfanin Dillancin Labarun xinhua na kasar Sin, ya ambato hukuma mai kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya tana cewa; Da akwai fiye da mutane 850,000, a kasar Afirka ta tsakiya, da su ke gudun hijira, da rabinsu kananna yara ne.
Rikice-rikicen da su ke faruwa a kasar ta Afirka ta tsakiya shi ne musabbabin yin hijirar mutanen kasar da dama, sai dai wasu da dama sun koma gida 2014.
A halin da ake ciki a yanzu, a cikin kasar wadanda suka bar gidajensu zuwa wasu garuruwa,sun kai 383,000 sai kuma wasu 486 da su ka shiga kasar Kamaru da Chadi da Jamhuriyar Congo.
Kungiyar ta Unicef ta kuma bayyana cewa; kananan yaran suna da bukatar makarantu da cibiyoyin bada magani da kuma tsaro a cikin kasar.