Afirka Ta Tsakiya ta bukaci Taimakon Duniya
Shugaban Kasar Afirka ta tsakiya ya bukaci taimakon Kungiyoyin kasa da kasa wajen farfado da yanayin tattalin arzikin kasar sa
A yayin buda taron bayar da taimakon na kungiyoyin kasa da kasa da ya gudana a birnin Bruxel na kasar Belguim a wannan Alkhamis, Shugaban Kasar Afirka ta tsakiya Faustin-Archange Touadéra ya bukaci taimakon kungiyoyin domin farfado da yanayin tattalin arzikin kasar sa.
Shugaban kasar Afirka ta tsakiyar ya gabatarwa mahalarta taron wani shiri na farfado da tattalin arzikin kasar da zai lagume tsabar kudi har dalar Amurka miliyar uku da miliyan 100 cikin shekaru biyar masu zuwa.watau daga shekarar 2017 zuwa 2021.inda ya kara da cewa cikin shekaru ukun farko shirin zai lakume $ miliyar daya da miliyan 600.
Mista Faustin-Archange Touadéra ya bayyana kyakkyawan fatan sa na samun taimako na kungiyoyin kasa da kasa domin cimma wannan shiri.
Kasar Afirka ta tsakiya ta fada cikin rikici ne tun bayan da 'yan tawayen saleka suka fara kai farmaki a cikin kasar.