Taron Brussels na Tallafawa Afirka ta tsakiya
Hukumomin da kasashen Duniya sun yi alkawarin tallafawa Janhuriyar Afirka ta Tsakiya domin sake farfadowa daga yakin basasa da ya daidaita kasar.
Shugaba Faustin-Archange Touadera ya yi kira ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji da su taimakawa Janhuriyar Afirka ta Tsakiya, daya daga cikin kasashe matalauta da ke kokarin farfadowa daga yakin basasa.
Ya jaddadawa mahalarta taron gidauniyar tallafawa kasar da ta gudana a birinin Brussels cewar, gudunmowar ta su za ta je nesa ba kusa ba wajen farfado da wannan kasa, inda ya gabatar da wani tsari da sai lashe tsabar kudi har dalar Amurka biliyan 3 da miliyan 100 a cikin shekaru biyar masu zuwa watau daga shekarar 2017 zuwa 2021 da nufin sake gina kasar da kuma farfado da tattalin arzikin ta.a cikin shekaru uku na farko tsarin zai lashe tsabar kudi kimanin biyar guda da milyan 100 na $.
Kasar Afirka ta tsakiya dai na daga cikin kasashe matalauta a Duniya, sabanin kabilanci da na addini ya jefa kasar cikin mawuyacin hali,kai har da ma kan iyakokin makwabtar kasar kamar su Jumhoriyar Demokaradiyar Kwango da Sudan ta kudu ya janyo musu rashin tsaro, rikici tsakanin 'yan tawayen Saleka da 'yan dabar Anti balaka ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare kuma da hijrar wasu dubai na daban.
Tun bayan faduwar Gwamnatin Fracois Bozeze a shekarar 2013, kasar Afirka ta tsakiyan ta fada cikin matsalar rashin tsaro, kasar Faransa ta yi amfani da wannan dama wajen tura Dakarun ta cikin kasar a kan da'awar cewa za su kare rayukan fararen hula, saidai Al'ummar kasar musaman ma musulmi da suka funkanci kisan gilla sun bayyana cewa shigar sojojin Faransa cikin kasar ya taimaka wajen kisan gillar da 'yan dabar Anti balaka suka yi musu, saboda a cewar su Sojojin Faransa na taimakawa 'yan dabar wajen basu kariya da makamai domin a gaban idanunsu a keyi musu kisan gilla ba tare da sun taimaka musu ba, a watan Janairun 2013 sojojin kasar Faransan suka shiga birnin Bangui kuma a ranar 30 ga watan Oktoban da ya gabata ne suka kawo karshen aikin su ba tare da sun cimma wata manufa ba, a cewar masu sharhi kan harakokin tsaro, Sojojin Faransa da Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da kuma na kasashen Afirka babu wata manufa da suka cimma a kasar Tsakiyar Afirkan.
Zaben Shugaban kasar da ya gudana a farkon wannan shekara ta 2016 a na iya cewa shi kadai nasarar da kasar ta samu bayan lafawar wannan rikici, A yayin da yake rantsuwar kama aiki, zababen shugaban kasar Faustin Archang Touadera ya yi alkawarin tabbatar da tsaro tare da medo da konciyar hankali a kasar, inda ya ce zai tattauna da kungiyoyin dake dauke da makamai domin su ajiye makaman su, amma har ya zuwa yanzu babu wani abu da ya tabbata a cikin alkawarinkan da Shugaban ya dauka. domin har yanzu a na ci gaba da kashe fararen hula a duk lokacin da wani rikicin ya taso tsakanin masu dauke da makaman.
A bagare guda a kwai kimanin Sojojin kasar Amurka kimanin dubu daya a kan iyakar kasar da kasar Sudan ta kudu, to saidai an kasa gane manufar su a wannan wuri, kare Al'ummar kasar ko kuma manufofin kasar Amurka, tahiri ya nuna cewa shigar Dakarun kasashen turai da Amurka ba hanyar kwarai ba ce wajen kawo karshen rikicin kasashen Afirka kamar yadda yake a kasar Afirka ta tsakiya, a halin da ake ciki dai a kwai Dakarun wanzar da zaman lafiya na MDD da ake kira da MINUSCA kimanin dubu goma, kuma sabuwar Gwamnatin kasar na da kyakkyawan fata ga Dakarun kasar ba tare da Dakarun kasashen waje ba su tabbatar da tsaro a fadin kasar.
Wannan taimako da Shugaban kasar ya gabatar, idan har manyan kasashe masu hanu da shuni da kuma kungiyoyin agaji suka ciki alkawarin da suka dauka na taimakawa kasar Afirka ta tsakiya, ana fatan cewa zai farkado da tattalin arziki, tsaro da kuma siyasar kasar.