Daruruwan Mutane Daga Yankin Arewa Maso Gabacin Kasar Congo Sun Kauracewa Gidajensu
Daruruwan mutanen gabacin kasar Congo sun arce daga yankunansu don kaucewa hare haren da yan tawaye suka fara kaiwa a yankin.
Tashar radio ta kasa da kasa na kasar Faransa ta bayyana cewa mutane kimani 800 ne suka kauracewa gidajensu a yankunan Mambasa da Ituri daga arewa maso gabacin kasar Congo De,ockradia bayan da yan tawaye suka fara kai hare hare a yankin kimani wata guda da ya gabata.
Labarin ya kara da cewa mutane a kauyukan Bafwasende da Avakubi da kuma Bafandu duk sun kauracewa kauyukan su sanadiyar hare haren da yan tawayen mau mau suke ta kaiwa a yankin.
Ana tuhumar yan tawayen Mau mau da kashe fararen hula a hare haren da suke kaiwa a wadan nan yankuna, sannan suna satar dukiyoyunsu