Harin Bam ya hallaka Sojojin Masar a tsibirin Sina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i14359-harin_bam_ya_hallaka_sojojin_masar_a_tsibirin_sina
Akalla Sojojin Masar takwas ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin bam a tsibirin Sina dake arewacin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:17+00:00 )
Nov 25, 2016 02:21 UTC
  • Harin Bam ya hallaka Sojojin Masar a tsibirin Sina

Akalla Sojojin Masar takwas ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin bam a tsibirin Sina dake arewacin kasar

A wannan Alkhamis ,wata Mota shake da bama-bamai ta tarwace a kusa da garin Al-Arish na yankin tsibirnin Sinai dake arewacin kasar Masar, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar Sojoji 8 tare da jikkata wasu da dama na daban.

A cikin 'yan makunin da suka gabata ne Dakarun tsaron Masar suka fadada kai farmaki a tsibirin Sinai din da nufin farautar kungiyoyin masu tsaurin ra'ayi, inda suka hallaka masu dauke da makamai da dama tare kuma da jikkata wasu na daban.

A halin da ake ciki, a kwai wasu kungiyoyin 'yan ta'adda da dama da suke gudanar da aiyukan su a tsibirin Sinai, mafi girma daga cikin su ita ce kungiyar Ansaru Baitil Makdis, bayan ta yi mubaya'a da kungiyar IS ta canza suna zuwa Wulayatu-Sinai.ita dai wannan kungiya ta sha kai hare-hare kan Dakarun tsaron Masar din a tsibirin Sinai.