Brundi: Sabon Kokarin Yin Sulhu
Shugaban Kasar Tanzania yana shiga tsakani domin samar da sulhu a kasar Brundi.
Shugaban Kasar Tanzania yana shiga tsakani domin samar da sulhu a kasar Brundi.
Tun a jiya laraba ne dai shugaba Benjamine Mkapa ya shiga kasar ta Brundi inda zai dauki kwanaki uku yana kokarin gano bakin zaren yin sulhu tsakanin gwamnati da 'yan hamayya.
Gabanin barinsa kasar Tanzania shugaba Mkapa, ya gabatar da shirinsa na kawo karshen rikicin da kasar ta Brundi ta ke fama da shi daga nan zuwa tsakiyar shekarar 2017.
Kasar Brundi dai ta fada cikin rikicin siyasa ne tun a 2015 da shugaba Peer Nkurinziza ya yi tazarce.
Kawo ya zuwa yanzu dai fiye da mutane 500 ne su ka rasa rayukansu yayin da wasu 600 zuwa 800 su ka bace. Wasu 300,000 kuma sun yi gudun hijira.