A sanar Makokin kwanaki uku a kasar Masar
(last modified Mon, 12 Dec 2016 05:20:43 GMT )
Dec 12, 2016 05:20 UTC
  • A sanar Makokin kwanaki uku a kasar Masar

Shugaban kasar Masar ya sanar zaman makoki na uku, bayan harin ta'addancin da aka kai wata majami'a a birnin alkahira

A cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi, Shugaban kasar Masar Abdulfatah Alsese ya yi Alwadai da harin ta'addancin da aka kai Majami'ar mabiyar Darikar Katolica a birnin Alkahira tare da bayyana kwanaki uku na zaman makwaki a fadin kasar gaba daya.

Alsese ya ce ta'addanci dukkanin Al'ummar kasar Masar ne ya shafa babu musulmi ko Kirista, to amma wannan hari a sanya Gwamnati  kara azama a yakin da take yi da ta'addanci.

A safiyar jiya Lahadi  ne  aka sanar da tashin wasu bama-bami  a cikin majami'ar Saint Marck da ke unguwar Abbasiyya a cikin birnin alkahira, harin da ya yi sanadiyar mutuwa da kuma jikkatar mutane da dama.

Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiya ko gungu da ya dauki alhakin wannan hari, a ranar juma'ar da ta gabata ma, jami'an 'yan sanda shida ne suka rasa rayukansu sanadiyar tashin Bam a garin Aljiza na kusa da birnin Alkahira.