Kibdawa sun bukaci Shugaban kasar Masar ya yi murabus
(last modified Wed, 14 Dec 2016 18:15:19 GMT )
Dec 14, 2016 18:15 UTC
  • Kibdawa sun bukaci Shugaban kasar Masar ya yi murabus

Bayan harin ta'addancin da aka kai Majami'ar su, 'yan kabilar Kibdawa na kasar Masar Sun bukaci Shugaba Alsese da ya yi murabus

Jaridar Al-Akhbar ta habarta cewa Kifdawan kasar Masar bayan harin da aka kai kan majami'ar Orthodox ta St Mark dake birnin Alkahira sun gudanar da zanga-zanga inda suka bukaci shugaban Kasar Abdulfatah Alsese da ya yi murabus daga mukaminsa.

Mahalarta zanga-zanga sun nuna fishin su ga Gwamnatin kasar tare da rera taken cewa Shugaban kasar ya kamata ka san kimar jinin Al'ummar Masar ka sauka daga kan mikaminka domin a daina zubar da jin bayan A...a kasar

A yayin jana'izar wadanda suka rasun, Dakarun tsaron kasar sun hana Mutane halartar jana'izar saidai wadanda suka samu goran gayyata.

A ranar Lahadin da ta gabata ne wani Bam ya tashi a majami'ar Orthodox ta St Mark dake birnin Alkahira inda Kibdawa 25 suka rasa rayukansu yayi da wasu 48 na daban suka samu raunuka.