An soki sabuwar dokar aikin jarida a kasar Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15595-an_soki_sabuwar_dokar_aikin_jarida_a_kasar_masar
'Yan Siyasa da 'yan jaridun kasar Masar sun bayyana cewa wannan sabuwar doka da Gwamnatin Masar din ta fitar za ta kayyade 'yancin fadar albarkin baki da na 'yan jaridu.
(last modified 2018-08-22T06:59:25+00:00 )
Dec 22, 2016 14:46 UTC
  • An soki sabuwar dokar aikin jarida a kasar Masar

'Yan Siyasa da 'yan jaridun kasar Masar sun bayyana cewa wannan sabuwar doka da Gwamnatin Masar din ta fitar za ta kayyade 'yancin fadar albarkin baki da na 'yan jaridu.

Kafar watsa labaran Pars ta habarta cewa 'yan siyasa da 'yan jaridun Masar sun soki sabuwar dokar da Gwamnati ta samar dangane da kafafen watsa labarai, inda suka ce wannan sabuwar doka za ta kayyade 'yancin fadar albarkin baki da na 'yan jaridu,bai kamata ba Majalisar dokokin kasar ta amince da wannan doka ba tare da mayar da ita ba zuwa ga kwamitin koli na kafafen yada labaran kasar ba. wasu kafafen yada labaran Masar sun habarta cewa wasu manbobin Gwamnati ne da suke adawa da 'yan cin kafafen yada labarai suka bijuro da wannan doka.

Sabuwar dokar dai ta baiwa Shugaban Kasa da majalisar zartarwa damar gyara da kuma canji na zaben manbobin Kwamitin kolin sadarwa a kasar, lamarin da 'yan siyasa ke ganin hakan zai yi babbar illa ga 'yancin fadar albarkatun baki da kuma 'yancin 'yan jarida.

Duk da cewa da dama daga cikin 'yan siyasar kasar sun bayyana adawarsu dangane da wannan sabuwar doka,a makun da ya gabata 'yan Majalisar Dokokin Masar din sun amince da ita,yanzu dai Shugaban kasar ta Masar na da karfin rusawa ko kuma gudanar da canje-canje tare da zaben sabin Shugabanin kwamitin koli na kafafen sadarwar kasar ba tare da izinin Majalisa ba.