Nijar : 'Yan Boko Haram Kimanin 30 Sun Mika Wuya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i15796-nijar_'yan_boko_haram_kimanin_30_sun_mika_wuya
Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun ce 'ya'yan kungiyar Boko Haram fiye da 30 sun mika wuya ga hukumomi a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:27+00:00 )
Dec 28, 2016 02:59 UTC
  • Nijar : 'Yan Boko Haram Kimanin 30 Sun Mika Wuya

Hukumomi a Jamhuriya Nijar sun ce 'ya'yan kungiyar Boko Haram fiye da 30 sun mika wuya ga hukumomi a yankin Diffa dake kudu maso gabashin kasar.

Ministan cikin gida na kasar ne Bazoum Mohamed ya bayyana hakan a shafinsa na Twetter yayin wata ziyara a Jihar ta Diffa mai iyaka da yankin arewa maso gabas na Najeriya da yayi fama da matsalar Boko Haram.

Wata majiyar tsaro ta shaidawa kanfanin dilanacin labaren AFP cewa yanzu haka ana rike  da mutanen da suka hada da maza 26 da mata uku a wata cibiyar tsaro dake jihar Diffa, kana akwai wata mata 'yar asalin kasar Najeriya da ita ma ta mika kan ta.

kafar gidan talabijin din kasar ya rawaito daya daga cikin tsaffin mayakan na Boko Haram yana mai cewa sun mika wuya ne saboda basu yarda da ayyukan kungiyar ba, saboda haka yanzu suna bukatar afuwa daga gwamnatin kasar don kada su sake shiga cikin irin wadanan kungiyoyi.

Wannan dai shi ne karo na farko da hukumomin Nijar suka ce wasu 'ya'yan kasar sun raba gari da kungiyar Boko haram dake kaiwa kasar hare-haren ta'addanci tun cikin watan Fabrairu na shekara 2015.