Nijar Za Ta Gaggauta Yiwa Masu Zargin Alaka Da Boko Haram Shari'a
-
Bazoum-Mohamed Ministan cikin gida na Jamhuriya Nijar
Gwamnatin Nijar ta ce zata gaggauta aiwatar da shirin yiwa wadanda ake tsare da yau sama da shekara guda bisa zargin alaka da kungiyar 'yan ta'adda ta Boko Haram shari'a.
Ministan cikin gida na kasar ne Bazoum Mohammed ya bayyana hakan a wannan Juma'a, yana mai cewa ga wadanda tuni aka far asaurarensu an kafa wani kwamiti inda alkalan shari'a zasu isa jihar Diffa domin gudanar da bincike a kauyukan da aka cafke mutanen, domin gaggauta matakin na shari'a.
Mista Bazoum ya bayyana hakan a gidan talabijin din kasar bayan wani ran gadi na kwanaki a jihar ta Diffa mai makoftaka da yankin arewa maso gabas na Najeriya wanda ya jima yana fama da matsalar Boko haram.
Wata majiyar tsaro ta shaidawa kanfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa kimanin mutane 1,200 da suka hada da 'yan Najeriya da Nijar ake tsare da tun cikin shekara 2015 bisa zarginsu da alaka da kungiyar Boko haram, aman har yanzu ba'a masu shari'a ba.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan da wasu 'yan kasar suka mika kansu ga hukumomin kasar bayan sun yanke alaka da lungiyar ta Boko haram, kuma bayan hakan ne gwamnatin Nijar ta dau matakin yin afuwa ga duk 'ya yan kasar da suka raba gari da kungiyar ta Boko haram.