An kashe Ministan Muhalli A Burundi
(last modified Sun, 01 Jan 2017 06:22:51 GMT )
Jan 01, 2017 06:22 UTC
  • An kashe Ministan Muhalli A Burundi

Rahotanni daga Burundi na cewa wani mutum da ba'a san ko wanene ba ko kuma manufarsa ya harbe har lahira ministan muhalli na kasar.

Lamarin dai ya auku ne a cikin tsakiyar daren Jiya wayewar wannan Lahadin a Bujumbura babban birnin kasar, kamar yadda hukumar 'yan sanda ta kasar ta sanar.

Mista Emmanuel Niyonkuru, dan shekaru 54 a duniya, wanda shi ne ministan kula da albarkatun ruwa da muhalli da tsare tsare na kasar ya gamu da ajalinsa ne bayan da wani dan bindiga ya harbe shi a daidai lokacin da yake kan hanyar komawa gidansa dake unguwar Rohero wajajen karfe 12h 45 na dare, kamar yadda kakakin 'yan sanda yankin Pierre  Nkurikiye ya sanar a shafinsa na Twitter.

Wannan kisan dai shi ne irinsa na farko da akayi wa wani minista dake kan mukaminsa tun dai bayan da kasar ta Burundi ta tsunduma cikin rikicin siyasa saboda yunkurin shugaba Pierre Nkurunziza na yin tazarce a wa'adi na uku a shekara 2015.