'Yan Boko Haram Sun Sake Mika Wuya A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16171-'yan_boko_haram_sun_sake_mika_wuya_a_nijar
Kimanin mayakan boko Haram ashirin ne a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar suka mika wuya ga hukumomi, kamar yadda ministan cikin gida na kasar ya sanar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jan 06, 2017 05:50 UTC
  • 'Yan Boko Haram Sun Sake Mika Wuya A Nijar

Kimanin mayakan boko Haram ashirin ne a jihar Diffa dake kudu maso gabashin kasar suka mika wuya ga hukumomi, kamar yadda ministan cikin gida na kasar ya sanar.

Wannan dai na zuwa ne kwanaki goma bayan da wasu mayakan na boko haram suka mika wuya ga hukumomin kasar.

Da yake bayyana hakan a wata hira ministan cikin gida na kasar Bazoum Mohamed ya ce kawo yanzu kimanin 'yan boko haram 50 ne suka mika wuya, wanda a cewarsa abun farin ciki ne.

Ministan ya kara da cewa za'a kara samun 'yan boko haram din dake mika wuya tare da jaddada cewa ai yakin da aka da kungiyar yama kare a wasu yankunan.