An Gama Shirye-Shiryen Rantsar Da Sabon Shugaban Ghana
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewar an gama dukkanin shirye-shiryen da ya kamata a gudanar wajen rantsar da sabon shugaban kasar Ghanan Nana Akufo-Addo da za a gudanar a safiyar gobe Asabar inda ake sa ran wasu shugabannin Afirka za su halarci biki.
Yayin da yake sanar da hakan, daya daga cikin shugabannin kamitin bikin rantsar da shugaban kasar Ghanan Ms Shirley Ayorkor Botchwey ta ce ana iya cewa an gama dukkanin shirye-shiryen da ya kamata a yi wajen rantsar da sabon shugaba Nana Akufo-Addo a gobe Asabar.
Ms Botchwey ta kara da cewa da safiyar gobe Asabar ne za a gudanar da bikin a dandalin Black Star Square da ke birnin Accra, babban birnin kasar Ghana inda a ke sa ran shugaban kasar Ivory Coast Mr. Alhasan Outarra shi ne zai zamanto babban bako.
Har ila yau daga cikin shugabannin kasashen da ake sa ran za su halarci bikin rantsar har da shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari. Fadar shugaban Nijeriya ta ce a safiyar gobe Asabar ne shugaba Buhari zai bar Abuja zuwa kasar Ghanan don halartar taron.
A gobe dai ana sa rana shugaba mai barin gado John Mahama na jam'iyyar National Democratic Congress (NDC) zai mika ragamar mulki ga zababben shugaba Nana Akufo-Addo na jam'iyyar New Patriotic Party (NPP) bayan da ya sha kaye a zaben da aka gudanar a watan Disamban da ya gabata.