Afirka Ta Tsakiya Ta Nemi Taimakon Kungiyoyi Kasa Da Kasa Akan Abinci
Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa domin magance matsa rashin abinci
Shugaban Kasar Afirka Ta Tsakiya Faustin-Archange Touadera ya bukaci taimakon kungiyoyin kasa da kasa domin magance matsalar rashin abinci.
Shugaba Faustin-Archange Toudera wanda ya ke magana akan rashin tsaron da kasarsa ta ke fuskanta ya yi ishara da yadda rashin abinci ya addabi kasar.
A shekarar 2016 da ta gabata, kungiyoyin kasa da kasa sun ware Euro biliyan biyu a wani taro da aka yi a watan Nuwamba a kasar Belgium, da zummar taimakawa kasar ta Afirka ta tsakiya.
Tun a cikin watan Decemba na shekarar da ta gabata ne dai, hukumar abinci ta duniya ta bayyana cewa; matukar ba ta sami taimakon abinci ba to za ta dakatar da taimakon da ta ke aikewa zuwa kasar Afirka ta tsakiya.