Burundi Ta Fara Shirin Janye Dakarunta A Somaliya
(last modified Wed, 18 Jan 2017 06:23:45 GMT )
Jan 18, 2017 06:23 UTC
  • EU ce ke da nauyin biyan Sojojin na Burundi
    EU ce ke da nauyin biyan Sojojin na Burundi

Fadar shugaban kasa A Burundi ta bukaci ma'aikatocin harkokin waje data tsaron kasar dasu fara aiwatar da shirin janye dakarun kasar dake cikin tawagar wanzar da zamen lafiya ta AMISOM a kasar Somaliya.

Mataimaki na farko na shugaban kasar Burundi Gaston Sindimwo, ya ce kasarsa ta umarci dakarun sojinta, dake aiki karkashin tawagar wanzar da zaman lafiya ta (AMISOM) da su janye daga tawagar.

Mr. Sindimwo ya ce hakan ya zama dole, duba da yadda ake kin biyan dakarun na Burundi kudaden alawus din su, alhali kuwa ana biyan takwarorin su na kasashen Uganda da Kenya. Ya ce ko shakka ba bu, ba wata kasa ta kirki da za ta lamunci irin wannan nuna wariya.

Mr. Sindimwo na wannan jawabi ne yayin wani taron manema labarai, inda ya kara da cewa, muddin kungiyar hadin kan Afirka ta AU ba za ta rika biyan dakarun kasar sa hakkin su yadda ya kamata ba, to kuwa mahukuntan Burundi za su umarce su, da su fice daga tawagar ta AMISOM tare da dukkanin kayan aikin su.