Shugaban Masar Ya Sake Bude Cibiyar Adana Kayan Tarihi Ta Birnin Alkahira
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i16804-shugaban_masar_ya_sake_bude_cibiyar_adana_kayan_tarihi_ta_birnin_alkahira
Shugaban kasar Masar Abdulfattah Al-Sisi ya sake bude babbar cibiyar adana kayan tarihin mulsunci da ke birnin Alkahira.
(last modified 2018-08-22T06:59:33+00:00 )
Jan 19, 2017 03:21 UTC
  • Shugaban Masar Ya Sake Bude Cibiyar Adana Kayan Tarihi Ta Birnin Alkahira

Shugaban kasar Masar Abdulfattah Al-Sisi ya sake bude babbar cibiyar adana kayan tarihin mulsunci da ke birnin Alkahira.

Jaridar Al-nahar ta bayar da rahoto a shafinta cewa, shugaba Al-sisi ya jagoranci bude wannan cibiya ne tare da wasu daga cikin manyan jami'an gwamnatin kasar Masar, da ma wasu baki daga kasashen ketare.

Tun daga shekara ta 2014 da aka kai wani harin bam a birnin Alkahira, aka rufe wannan babbar cibiyar kayan tarihin muslunci, wadda tana daya daga cikin wuraren adana kayan tarihi mafi muhimmanci a duniya, sakamakon lalacewar wani bangaren ginin cibiyar.

Wannan cibiya na daga cikin cibiyoyin da masu bincike daga kasashen duniya suke gudanar da ayyukan bincike a cikinta, baya ga kayan tarihin muslunci, akwai wasu abubuwa na daban da tarihinsu ke koma zuwa ga dubban shekaru da suka gaba.

Daga cikin kasashen da suka dauki nauyin aikin gyaran wannan cibiya akwai Amurka, UAE, Switzerland, Italia da kuma UNESCO.