Jami'an Tsaron Maroko Sun Yin Nasarar Rusa Wata Kungiyar Ta'addanci A Kasar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17113-jami'an_tsaron_maroko_sun_yin_nasarar_rusa_wata_kungiyar_ta'addanci_a_kasar
Ma'aikatar harkokin cikin gidan Moroko ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wata kungiyar 'yan ta'adda tare da rusata.
(last modified 2018-08-22T06:59:36+00:00 )
Jan 28, 2017 08:16 UTC
  • Jami'an Tsaron Maroko Sun Yin Nasarar Rusa Wata Kungiyar Ta'addanci A Kasar

Ma'aikatar harkokin cikin gidan Moroko ta sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wata kungiyar 'yan ta'adda tare da rusata.

A bayanin da ma'aikatar harkokin cikin gidan Maroko ta fitar a jiya Juma'a yana dauke da cewa: Jami'an tsaron kasar sun yi nasarar gano wata kungiyar ta'addanci da take da rassa a gariuruwan El-Jadidah, Sale, El-Gara da Boulaouane da suke fadin kasar, inda suka yi nasarar kame mambobin kungiyar bayan gudanar da bincike mai zurfi kan ayyukan kungiyar.

Bayanin ya kara da cewa: Kungiyar ta'addancin tana karbar umurni ne daga manyan 'yan ta'addan kungiyar Da'ish da suke kasashen Siriya, Iraki da Libiya, kuma tuni ta fara shirin aiwatar da hare-haren wuce gona da iri a kasar ta Maroko.

Har ila yau a yayin binciken an gano tarin makamai, na'urorin sadarwa da jigiden bama-bamai na kai hare-haren kunan bakin wake, baya ga kananan makamai irin wukake da adduna.