Masar Da Habasha Za Su Duba Batun Badakalar Madatsar Ruwa Ta Nahdha
Bangarorin Masar da Habasha za su duba hanyoyin da ya kamata su bi domin kawo karshen badalakar da ke tsakaninsu a kan batun ginin madatsar ruwa ta Nahdha a Habasha.
Kamfanin dillancin labaran Iran ya habarta cewa, shugaban kasar Masar Abdulfattah Sisi da kuma Firayi ministan kasar Habasha Hailemariam Desalegn, sun tattauna kan badakalar da ke tsakanin kasashensu dangane da batun ginin madatsar ruwa ta Nahdha, da kuma yadda za a warere matsalar ta hanyar fahimtar juna.
Bangarorin biyu sun tattauna wannan batu a daidai lokacin da Masar take zargin gwamnatin Saudiyyah da hannu wajen kara tunzura Habasha kan batun ginin madatsar ruwan ta Nahdha, inda Saudiyya ke shirin bayar da wasu biliyoyin daloli domin kammala aikin, dawanda hakan zai kawo babban cikas ga harkokin noma rani a kasar Masar.