Sojojin Majalisar Dinkin Duniya Sun Kai Hare Hare A Afrika Ta Tsakiya
(last modified Mon, 13 Feb 2017 06:19:29 GMT )
Feb 13, 2017 06:19 UTC
  • Sojojin Majalisar Dinkin Duniya Sun Kai Hare Hare A Afrika Ta Tsakiya

Labaran da suke fitowa daga Afrika ta Tsakiya sun bayyana cewa sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar dinkin duniya sun yi barin wuta kan wata kungiyar yan tawaye a kusa da garin Bambari sun kuma kashe wasu daga cikinsu.

Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto majiyar dakarunMINUSCA tana cewa mayakan kungiyar Popular Front for the Renaissance of Central African Republic (FPRC) sun ketara iyakan da suka sanya masu kusa da garin don haka aukuwar fada a tsakanin kungiyoyin yann tawaye a garin, don haka ne jirgin yakin rundunar mai saukar ungulu ya yi barin wuta kan mayakan wannan kungiyar don hana su isa gasar. inji Vladimir Monteiro. kakakin rundunar.

Yayan kungiyar FPRC dai basa dasawa da wata kungiyar ta kabilar Fulani mai suna Union for Peace in Central Africa (UPC) don haka ne ma a fadar su ta bayan mayakan na FPRC suka shiga gida gida a garin Bambari suna zakulo yayan wannan kabila suka kashewa. 

Kasar Afrika ta tsakiya ta fada cikin yakin basasa a shekara ta 2013 bayan da kungiyar seleka ta hambarar da gwamnatin Fransua buzize daga kan kujerar shugabancin kasar.