Sukar Hukumar Zaben Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.
(last modified Mon, 13 Feb 2017 12:05:46 GMT )
Feb 13, 2017 12:05 UTC
  • Sukar Hukumar Zaben Kasar Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Radiyon Faransa na kasa da kasa ya ambato mai sa ido akan hukumar zaben Demokradiyya Congo gustave omba bindimono yana yin suka akan tsarin hukumar zaben.

Radiyon Faransa na kasa da kasa ya ambato mai sa ido akan hukumar zaben Demokradiyya Congo gustave omba bindimono yana yin suka akan tsarin hukumar zaben.

gustave omba bindimono ya yi ishara da cewa kawo ya zuwa yanzu, mutane miliyan 13 masu kada kuri'a ne aka yi wa rijista, abinda ya ke nuni da rashin kayan aiki na hukumar.

Haka nan kuma ya yi suka rashin bayyana yadda ake amfani da kudade a cikin hukumar.

Tun a 2015 ne aka bude rijistar masu kada kuri'a a kasar ta Demokradiyyar congo.

Yarjejeniyar da aka cimmawa a tsakanin yan siyasar kasar ta Demokraiyyar Congo, Shugaba Kabilla zai ci gaba akan kujerar mulkinsa har zuwa karshen wannan shekarar ta 2017.