Cote De Voire: Jami'an Tsaro Sun kama 'yan jarida 6.
(last modified Tue, 14 Feb 2017 06:34:15 GMT )
Feb 14, 2017 06:34 UTC
  • Cote De Voire: Jami'an Tsaro Sun kama 'yan jarida 6.

Babban mai shigar da kara na kasar ta Cote De Voire ya sanar a jiya litinin cewa; An Kame 'yan jaridar ne saboda fitar da wasu bayanai na sirri masu alaka da boren da jami'an tsaron kasar su ka yi.

Babban mai shigar da kara na kasar ta Cote De Voire ya sanar a jiya litinin cewa; An Kame 'yan jaridar ne saboda fitar da wasu bayanai na sirri masu alaka da boren da jami'an tsaron kasar su ka yi.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya nakalato babban mai shigar da kara na kasar ta Cote De Voire yana ci gaba da cewa; Manufar 'yan jaridar shi ne ingiza sauran jami'an tsaron kasar da su ke a birnin Abidjan da su ma su yi bore.

A ranar juma'ar da ta gabata ne gwamnatin kasar ta yi zama da wakilan sojojin da su ka yi bore a cikin garuruwa daban-daban na kasar domin tattauna matsalolinsu.

Tags