Nijar Ta Sanar Da Murkushe Cutar Zazzabin Rift Valley
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17670-nijar_ta_sanar_da_murkushe_cutar_zazzabin_rift_valley
Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijar ta sanar da shawo kan cutar zazzabi Rift Valley dake yaduwa daga dabbobi zuwa mutane.
(last modified 2018-08-22T06:59:41+00:00 )
Feb 15, 2017 02:24 UTC
  • Nijar Ta Sanar Da Murkushe Cutar Zazzabin Rift Valley

Hukumomin kiwon lafiya a Jamhuriyar Nijar ta sanar da shawo kan cutar zazzabi Rift Valley dake yaduwa daga dabbobi zuwa mutane.

A sanarwar data fitar Jiya Talata ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce t ba'a samu wani sabon mutum da ya kamu da cutar  tun a watan Oktoba na bara zuwa yanzu.

Ministan kiwon lafiya na kasar ya bayyana a gun taron manema labaru cewa tun daga ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2016, babu sabon mutumin da ya kamu da cutar zazzabi na Rift Valley ba a dukkan kasar.

Bisa ma'aunin kasa da kasa, an riga an kawo karshen cutar a kasar ta Nijar,  amman hukumomin sun yi kira ga jama'ar kasar da su yi takatsantsan don kaucewa sake bullar cutar.

Mutane a kalla 33 ne cutar ta zazzabin Rifta Valley ( fievre du Rifft) ta kashe a NIjar cikin kimanin 400 da suka kamu da ita a yankin Tchintabaraden dake jihar Tawa a tsakiyar kasar.