Gwamnatin Burundi Ta Haramta Tattaunawa Don Warware Matsalolin Kasar
Gwamnatin kasar Burundi ta bada sanarwan cewa ba zata halarci taron tattauna shawo matsalolin kasar wanda aka bude a yau a kasar Tanzania ba.
Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto kakakin fadar shugaban kasan Burundi Philippe Nzobonariba yana fadar haka a yau Alhamis ya kuma kara da cewa a taron sulhuntawa na tanzania akwai wasu da suka halarci tattaunawan amma kuma a nan Burundi ana nemansu don laifuffuka da suka aikata.
Mr Philippe Nzobonariba ya kara da cewa ba abinda taron Tanzania karkashin shugabancin tsohon shugaban kasar zai kara sai kara lalacewa. Don haka don haka gwamnatinsa ta haramta taron ba zata kuma halarceta ba.
Tun shekara ta 2015 ne shugaban kasar Burundi Peir Nkroziza ya shiga takara karo na ukku a zaben shugaban kasar wanda hakan ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar. Sannan daga lokacin ne rikicin siyasa ta bullo a kasar ta kuma yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 500 sannan wasu kimani dubu 300 suka kauracewa kasar , suka shiga kasar Uganda ko kuma Democradiyyar Congo.