Masar Ta Hana Wasu Jami'an Diblomasiyyar Amurka Da Turai Shiga Kasarta
Gwamnatin kasar Masar ta hana jami'an diblomasiyyar kasashen Turai guda ukku don maida martani ga wadan nan kasashe.
Kamfanin dillancin labaran Atonoly na kasar Turkia ta nakalto majiyar tashar jiragen sama na Alkahira a jiya jumma'a tana cewa an hana Angela Katrina wani jami'in diblomasiyyar Britania a kasar Ukrain, David Maldireen Jami'in diblomasiyyar kasar Amurka a kasar Saudia da kuma Jasteen James Jami'in diblomasiyyar Amurka a Palastinu shiga kasar Masar ba tare da visa ba, don suna rike da Passport na diblomasia.
Ya zuwa yansu dai ofisoshin jakadancin kasashen Amurka da Britania a birnin Alkahira basu maida martani ba.
Gwamnatin kasar Masar ta fara daukar irin wadan nan matakai na ramawa kamar byadda aka yi mata tun shekara ta 2010M.