Masar: An Kashe Wani Kusa Na Kungiyar Da'esh a Yankin Sina
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i17776-masar_an_kashe_wani_kusa_na_kungiyar_da'esh_a_yankin_sina
Majiyar Tsaron Kasar Masar ta ce an kashe daya daga cikin kusoshin kungiyar 'yan ta'adda ta "Ansaru Baitul Mukaddas" a gundumar sinna ta arewa.
(last modified 2018-08-22T06:59:42+00:00 )
Feb 18, 2017 15:36 UTC
  • Masar: An Kashe Wani Kusa Na Kungiyar Da'esh a Yankin Sina

Majiyar Tsaron Kasar Masar ta ce an kashe daya daga cikin kusoshin kungiyar 'yan ta'adda ta "Ansaru Baitul Mukaddas" a gundumar sinna ta arewa.

Majiyar Tsaron Kasar Masar ta ce an kashe daya daga cikin kusoshin kungiyar 'yan ta'adda ta "Ansaru Baitul Mukaddas" a gundumar sinna ta arewa.

Tashar telbijin din Skynews wacce ta nakalto majiyar tsaron kasar ta Masar, ta ci gaba da cewa dan'ta'addar da aka kashe mai suna Hamad Salim Sullaiman dan shekaru 30.

Majiyar tsaron ta ci gaba da cewa; wanda aka kashe din yana da hannu wajen kashe sojojin masar 5 a ranar 23 ga watan Janairu na wannan shekara a yayin da su ke komawa gida daga wurin aiki domin yin hutu.

Yankuna daban-daban na gundumar Sina ta arewa na fuskantar hare-haren ta'addani akan sojojin kasar.