Rikicin tsakanin masu Zanga-zanga da Jami'an tsaro a kasar Guinee Conakry.
Gwamnatin Kasar Guinee ta sanar da mutuwar mutane sanadiyar taho mu gama tsakanin masu zanga-zanga da Jami'an 'yan sanda a birnin Conakry fadar milkin kasar
A wata sanarwar da ta fitar, Gwamnatin kasar Guinee ta ce taho mu gaman da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da jami'an 'yan sanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 5 tare da jikkata wasu sama da 30 a jiya Litinin.Har ila yau Sanarwar ta tabbatar da cabke wasu matasa 12, wadanda yanzu haka ke amsa tambayoyi a Ofishin jami'an 'yan sanda.
Zanga-zangar da aka yi jiya Litinin ta yi sanadiyar rufe shaguna da ksuwanin birnin, yanzu haka dai rahotanin sun nuna cewa an samu konciyar hali na dan wani lokaci bayan da jami'an tsaro na jandarma da Sojoji suka shiga cikin lamarin.
Mahalarta zanga-zangar dai sun bukaci Gwamnati da ta gaggauta buda Makarantu bayan da aka rufe su makuni uku da suka gabata.