Goyon bayan Nijer a kan yaki da ta'addanci
(last modified Thu, 23 Feb 2017 10:53:07 GMT )
Feb 23, 2017 10:53 UTC
  • Goyon bayan Nijer a kan yaki da ta'addanci

Shugaban Kasar Nijer ya bayyana goyon bayan kasar sa a kan yaki da ta'addanci da kuma masu tsatsaurar akida a yankin

Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto Shugaban kasar Nijer Alh Mahamadu Issoufou a yayin da yake ganawa da wata tawaga ta wakilan MDD da Kwamitin yaki da ta'addancin na Kwamitin tsaron MDD a marecen jiya Laraba na cewa kasar sa na fuskantar hare-haren ta'addanci na kungiyar Boko haram a gabashin kasar da kuma hare-haren 'yan ta'adda a kan iyakar kasar da Mali da kuma iyakar kasar da Libiya.

A nasa bangare  Mohamed Ibn Chambass wakilin musaman na MDD a yammacin Afirka wanda kuma shi ne ya jagoranci wannan tawaga ya ce karfafa alaka da kuma aiki tare tsakanin MDD da kasashen Yammacin Afirka na yankin Sahel wajen yaki da ta'addanci zai kasance bisa jagorancin kasar ta Nijer.

Tun daga farkon shekarar 2015 ne kasar ta Nijer ta fara fuskantar hare-haren ta'addanci na mayakan kungiyar Boko haram a kudu maso gabashin kasar.