Nijar : Kungiyar Alkalai Ta Bukaci A Gurfanar Da Ministan Kudi
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18024-nijar_kungiyar_alkalai_ta_bukaci_a_gurfanar_da_ministan_kudi
Kungiyar alkalai ta kasa a Nijar ta bukaci ministan kudi na kasar Hasumi Masa'udu da ya mika kansa ga kotu domin yin bayyani akan badakalar nan ta gano wasu makuden kudade na Urenium da aka zuba a wani banki a Dubai da aka ambato sunansa.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Feb 25, 2017 14:05 UTC
  • Nijar : Kungiyar Alkalai Ta Bukaci A Gurfanar Da Ministan Kudi

Kungiyar alkalai ta kasa a Nijar ta bukaci ministan kudi na kasar Hasumi Masa'udu da ya mika kansa ga kotu domin yin bayyani akan badakalar nan ta gano wasu makuden kudade na Urenium da aka zuba a wani banki a Dubai da aka ambato sunansa.

A cikin wata wasika da ta aikewa manema labarai kungiyar ta SAMAN ta ce dole fa Minista Hasumi ya daina kewaye kewaye ya fito ya yi murabus ya kuma mika kansa ga kotu domin yin bayyani akan wannan badakala wace ita kadai ce hanyar da zata fitar dashi idan fa baya da hannun a ciki.

Idan kuma ba hakan ba a cewar kungiyar to nauyi ne daya rataya akan shugaban kasar Isufu Mahamadu da ya tube ministan ya kuma mika shi ga kotu ya fuskanci shari'a akan wannan badakala ta karkata kudaden gwamnatin kasar.

A baya bayan nan ne dai wata jaridar mai suna ''Le Courier a kasar ta Nijar ta bankado labarin cewa kanfanin AREVA mai hakar karshen Urenium a a Nijar din ya zubawa gwamnatin kasar zunzurutan kudade da yawan su ya kai Bilyan 200 na CFA a wani banki dake Dubai a shekara 2012.

To sai dai Hassoumi Massaoudou daraktan ayyukan mulkin fadar shugaban kasar a wancan lokaci sannan kuma ministan kudi a yanzu, ya ce ba haka zance yake ba.

Wannan lamarin dai ya tayar da zazafar muhawara tsakanin al'ummar kasar ta Nijar a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Isufu Mahamadu ta kaddamar da shirin nan na ta mai suna ''Mai Bulala'' wanda ya tanadi matakin ba sani ba sabo akan duk wani mahaluki da zakulo duk wani da ya yi rubda ciki da dukiyar kasa, batun da ma a cen baya ke shan suka akan cewa na bita da kulin siyasa ne.