Daurin Shekaru 5 A Kan Wani Malamin Masar Bisa Zargin Tozarta Muslunci
Wata kotu a kasar masar ta zartar hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso a kan wani malmin addini mai suna Muhammad Abdullah da aka fi sani da sheikh Mizo, bisa zarginsa da tozarta ababe masu tsarki a muslunci.
Shafin yada labarai na Alhurra ya bayar da rahoton cewa, kotun birnin Shibra Alkhaima da ke cikin gundumar Kailubiyya ta yanke hukuncin daurin shekaru 5 a gidan kaso a kan sheikh Mizo, bayan da ya nuna rashin amincewarsa da wasu daga cikin hadisan manzo ingantattu a wajen ahlu sunna, inda kotun ta ce hakan yana a matsayin tozarta hadisan manzo ne.
Jim kadan bayan yanke hukuncin, kotun ta bayar da umanin a tsare sheikh Mizo a gidan kason Shibra Alkhaimah, domin ya yi zaman kaso a wurin, amma bayan sanar da hukuncin daurin shekaru 5 a kansa, sheikh Mizo ya fara yajin cin abinci.
A kwanakin bayan ne malamin ya ce shi ne Mahdi da aka yi alkawalin zai bayyana a karshen duniya, kuma yana kiran dukkanin musulmi sunnah da shi'a da su yi masa mubaya'a, furucin da ya fusata da dama daga cikin malaman addini a kasar Masar.