Yunkurin kara wa'adin Shugaban kasa a Masar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18084-yunkurin_kara_wa'adin_shugaban_kasa_a_masar
A ci gaba da kokarin Masar na samun karin karfi a cikin gida da yankin, Wakilan Majalisar dokokin kasar na yunkurin kara wa'adin Shugaban kasa daga shekaru 4 zuwa 6.
(last modified 2018-08-22T06:59:45+00:00 )
Feb 28, 2017 02:31 UTC
  • Yunkurin kara wa'adin Shugaban kasa a Masar

A ci gaba da kokarin Masar na samun karin karfi a cikin gida da yankin, Wakilan Majalisar dokokin kasar na yunkurin kara wa'adin Shugaban kasa daga shekaru 4 zuwa 6.

A yayin da yake ishara kan rashin isar lokaci na Shugaban kasa wajen gudanar da shirinsa a shekaru 4, Isma'il Nasrudindin wani dan Majalisar Dokokin kasar Masar ya bayyana cewa 'yan Majalisu sun fara tattara sanya hanu da nufin canza kundin tsarin milkin kasar wanda zai kara wa Shugaban kasar karfi iko, wannan yunkuri na 'yan majalisar kasar Masar na zuwa ne a yayin da alkaluma ke bayyana cewa sama da kashi 70% na Al'ummar kasar na adawa da ci gaban zaman Shugaba Alsese a kan karagar milki.

Abin tuni a nan shi ne Majalisar dokokin ta Masar ta kafu ne bayan da Shugaba Abdulfatah Alsese ya dare kan karagar milki, lamarin da ya sanya ta kasance mai goyon bayan sa ido rufe duk kuwa da irin adawar da 'yan kasar ke nunwa.bayan nuna goyon bayan sa na tsayawa takarar Shugabancin kasar a shekarar 2018, magoya bayan Shugaba Alsese na ci gaba da tattara sanya hannu domin yiwa kundin tsarin milkin kasar kwaskwarima wanda zai kara masa wa'adin zama kan karagar milki daga shekaru 4 zuwa 6.

A shekarar 2013 ne Shugaba Alsese ya dare kan karagar milkin kasar ta Masar bayan da ya yiwa Zababan Shugaban kasar Muhamad Mursi juyin milki, a cikin kwanakin baya-bayan nan Shugaban kasar ta Masar ya samar da wasu sabin dokoki da suka yi garan bawul da yancin 'yan Jaridu da kungiyoyin fararen hula, lamarin da wasu 'yan kasar ke ganin cewa mataki ne na milkin kama karya kamar yadda ya kasance a Gwamnatin tsohon Shugaban kasar na milkin Soja Husni Mubarak.a cikin irin wannan yanayi 'yan Majalisar dokokin kasar ke yunkurin karawa Shugaban kasar karfin iko da kuma karin wa'adi na zaman kan karagar milki, ko da yake hakan na bukatar gudanar da bincike a ciki da wajen kasar.

A bangare guda wasu 'yan Siyasar kasar na ganin cewa take-taken na Shugaban kasar da magoya bayan sa na canza kundin tsarin milki da zai karawa Shugaban kasar karfin iko a bangare daban daban da kuma kara masa wa'adin zama kan karagar milki wani yunkuri na bashi damar dawwama  a kan karagar milkin kasar.

A halin da ake ciki kasar ta Masar na kokarin samun karfin fada a ji a yankin, kuma wannan yunkuri na Shugaba Al-Sise irin sa ne takwarsa Ordugan na kasar Turkiya ke yi domin samun karfin fada a ji a yankin da kuma dawwama a kan karagar milki.inda yanzu haka Shugabanin biyu ke ci gaba da neman goyon bayan wasu kasashen Yamma kamar su Birtaniya da Amurka.

Saidai masana harakokin siyasar kasar na ganin cewa yunkurin Shugaban kasar ta Masar ya yi hanun riga da bukatar yunkurin juyin juya halin shekarar 2011a kasar, inda Al'ummar Masar din suka tashi domin neman canji da kuma samar da Gwamnatin da za ta jagoranci kasar bisa bukatar Al'ummar kasar.