Nijar : An Kafa Dokar Ta Baci A Wasu Yankuna 7
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18218-nijar_an_kafa_dokar_ta_baci_a_wasu_yankuna_7
Gwamnatin Nijar ta kafa dokar ta baci a wasu yankuna bakwai dake kan iyaka da kasar Mali, sakamakon barazanar ayyukan ta'addanci da al'umma yankunan ke fuskanta.
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 04, 2017 07:11 UTC
  • Nijar : An Kafa Dokar Ta Baci A Wasu Yankuna 7

Gwamnatin Nijar ta kafa dokar ta baci a wasu yankuna bakwai dake kan iyaka da kasar Mali, sakamakon barazanar ayyukan ta'addanci da al'umma yankunan ke fuskanta.

Yankunan sun hada da Walam, Ayoru, Bankilare, Abala da kuma Banibongu a jihar Tillaberi, sai kuma Tassara da Tillia a jihar Tawa.

Ko bayan ga hakan gwamnatin kasar ta tsawaita dokar ta bacin data kafa a jihar Diffa mai fuskantar barazanar Boko Haram.

Gwamnatin dai ta dau wannan matakin ne a yayin taraon majalisar ministocinta na jiya Juma'a 

Wannan dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan harin da wasu mayakan jihadi da ake kautata zaton na MUJAO ne daga Mali suka kaiwa sojojin kasar Hari a yankin Intirziwane na Wallam inda sojojin kasar akalla 15 suka rasa rayukansu.