'Yan Adawa Sun yi gagarumar zanga-zanga a Nijer
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18222-'yan_adawa_sun_yi_gagarumar_zanga_zanga_a_nijer
Dubban magoya bayan kawancen jam'iyyun adawa na FRDD a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da gagarumar anga-zanga a harabar majalisar dokokin kasar dake Niamey fadar milkin kasar
(last modified 2018-08-22T06:59:46+00:00 )
Mar 04, 2017 14:11 UTC
  • 'Yan Adawa Sun yi gagarumar zanga-zanga a Nijer

Dubban magoya bayan kawancen jam'iyyun adawa na FRDD a Jamhuriyar Nijar sun gudanar da gagarumar anga-zanga a harabar majalisar dokokin kasar dake Niamey fadar milkin kasar

Rahotanni daga birnin Yamai din sun bayyana cewa mahalarta zangar-zangar na dauke da kwalaye dauke da rubuce-rubuce, inda  suke zargin gwamnatin kasar da rashin iya mulki da kuma yadda cin hanci da rashawa da yayi wa  gwamnatin katutu.

Kawancen adawar sun bayar da misali da wata almundahana da ake zargin ministan kudin kasar Hasoumi Masa'udu ya yi da kudade biliyar dari biyu na CEFA a wata harka ta ma'adanin Uranium, a lokacin yana matsayin darakta a fadar shugaban kasa.Sun ce gwamnatin ta ki yin komai game da wannan zargi, duk da kiraye-kirayen da ake yi.

Rahotanni na cewa an dade ba a yi irin wannan zanga-zangar ba a kasar ta Nijar, ta fuskar yawan jama'a da suka fito. To sai dai zanga-zangar ta  gudana ne cikin lumana kamar yadda aka tsara.

har ila yau mahalarta zanga-zangar sun bukaci Gwamnati da ta saki fursunonin siyasa da ake rike da su tun a shekarar 2015 kan zargin yunkurin juyin mulki, sannan sun bukaci ficewar dakarun Faransa da Amurka da Jamus da suka kafa sansanonin yakar ‘yan ta’adda a Mali da Libya.