Nijar: 'Yan Boko Haram 130 Suka Mika Wuya
A jamhuriya Nijar 'yan boko haram 130 ne suka mika wuya ga hukumomin kasar tun bayan da gwamnatin kasar ta shelanta yin ahuwa ga duk wani dan kasar da ya tuba ya raba gari da kungiyar.
Shugaban kasar Alhaji Isufu Mahamadu ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da wakilan kwamitin tsaro na MDD dake ran gadi a yankin tafkin Chadi, a yayin da suka isa Yamai fadar gwamnatin ta Nijar.
Shugaba Isufu ya bayyana cewa daga watan Disamba bara ya zuwa yanzu an samu 'yan boko haram din 130 da suka ajiye makamai suka mika kansu ga hukumomin kasar, lamarin da a cewarsa yake tabbatarda da cewa an ci nasara kan kungiyar ta Boko Haram.
A ranar Juma'a data gabata ce wata tawagar wakilan kwamitin sulhu na MDD mai mambobi 15 ta fara ziyara a yankin tafkin Chadi domin janyo hankalin duniya akan irin mumunan halin da ake ciki a wannan yankin.
A jiya dai tawagar ta isa birnin Maiduguri na Najeriya, domin duba halin da ake ciki kan matsalolin da ake fuskanta sakamakon ayyukan kungiyar Boko Haram.