'Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an Tsaron Nijar Hudu
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18284-'yan_ta'adda_sun_kashe_jami'an_tsaron_nijar_hudu
Rahotanni daga Nijar na cewa akalla jami'an tsaron Jandarman kasar hudu ne suka rasa rayukansu a yayin wani hari da ake kautata zaton 'yan ta'adda sun kai masu a yankin Wanzarbe dake jihar Tillaberi.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 06, 2017 13:46 UTC
  • 'Yan Ta'adda Sun Kashe Jami'an Tsaron Nijar Hudu

Rahotanni daga Nijar na cewa akalla jami'an tsaron Jandarman kasar hudu ne suka rasa rayukansu a yayin wani hari da ake kautata zaton 'yan ta'adda sun kai masu a yankin Wanzarbe dake jihar Tillaberi.

Wata majiyar tsaro data bukaci a sakaya sunanta ta shaidawa kanfanin dilancin labaren faransa na AFP cewa 'yan bindigan sun kaiwa jami'an tsaron  hari ne a cikin daren jiya a barikinsu dake gundumar ta Wanzarbe a jihar Tillaberi dake yammacin kasar a kusa da kasashen Mali da Burkina Faso.

Alkalumma dai sun nuna cewa akalla sojojin Nijar 43 ne suka gamu da ajalinsu a jerin hare haren ta'addancin da  kasar ta fuskanta daga watan Oktoban bara zuwa watan nan na Fabrairu da muke ciki a jihohin Tillabery da Tawa dake raba iyaka da kasar Mali. 

A makon daya gabata ne gwamnatin Nijar ta ayyana dokar ta baci a wasu gundumumi bakwai na wadannan jihohin dake fuskantar barazana 'yan ta'adda.

Wannan harin dai ya ci karo da wanda wasu mayakan jihadi suka kai akan iyakar kasashen Mali da Burkina faso a cikin daren jiya inda suka kashe sojojin Mali 11.