Burundi : An Nemi A Kakabawa Masu Keta Hakkin Bil Adama Takunkumi
(last modified Wed, 08 Mar 2017 16:35:57 GMT )
Mar 08, 2017 16:35 UTC
  • Burundi : An Nemi A Kakabawa Masu Keta Hakkin Bil Adama Takunkumi

Kungiyoyi masu zamen kansu na gida dana ketare a Burundi,sun bukaci kwamitin tsaro na MDD da ya kakabawa masu keta hakkin bil adama takunkumi.

Kungiyoyi 19 ne suka sanya hannu akan wannan bukata ciki har da kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa (HRW) da kuma ta 'yan jaridu marar iyaka (RSF).

Kungiyoyin sun ce ire-iren wadanan matakan kamar hana tafiye-tafiye da toshe kadarori zai zamo babban darasi ga jami'an gwamnatin ta Burundi dake muzgunawa al'ummominsu.

Wannan kiran dai na zuwa ne a yayin da kwamitin tsaro na MDD zai tattauna halin da ake ciki a kasar ta Burundi dake shan suka daga ire iren wadanan kungiyioyin akan yadda jami'an gwamnati ke ci gaba da keta hakkin dan adam.

An dai dade ana zargin gwamnatin Burundi da cin zarafin bil adama wanda ya yi kamari tun bayan da shugaban kasar Pierre Nkurinziza ya bayyana aniyarsa ta yin tazarce, saidai sau tarin yawa gwamnatin na musunta hakan.