Amurka ta kori 'yan kasar Somaliya daga cikin kasar
'yan kasar Somaliya da dama ne aka mayar da su birnin Magadushu daga kasar Amurka
A cikin wata sanarwa da Ministan tsaron gida na kasar Somaliya Abdulrazak Umar Muhamad ya fitar a wannan juma'a ya ce tun bayan sabuwar dokar da Shugaban Amurka Donal Trump ya sanya wa hannu, wannan shi ne karo na biyu da ake tiso gyeyar 'yan kasar daga Amurka sannan kuma ya ce 'yan kasar kimanin 70 da aka dawo da su gida, sun kwashe sama da shekaru biyu suna rayuwa a kasar ta Amurka.
Ministan tsaron gidan Somaliyan ya kara da cewa Ofishin Jakadancin kasar ne da Gwamnatin Amurka suka cimma matsaya kan dawo da wadannan mutane gida, kuma yanzu haka Ofishin na su na bin hanyoyin saukakewa 'yan kasar masu son komowa gida, su dawo cikin sauki.
Bisa sabuwar doka da Shugaba Trump ya sanyawa hanu a kan 'yan hijra,za a dakatar da bayar da Visa wato takardar izinin shiga Amurka ga 'yan kasashen Iran, Somaliya, Sudan, Yemen, Siriya gami da Libiya har na tsahon wattani uku, kuma har zuwa kwanaki 120 ba za a bayar da dama ga 'yan gudun hijra shiga cikin kasar ba.