Gabon: Yan Hamayya Sun Yi Watsi Da Gayyatar Gwamnati
Jagoran yan hamayyar 'yan siyasar kasar ta Gabon, Jean Ping, ya ce; Ba za su shiga cikin tattaunawar da shugaban kasa ya gayyace su ba.
Jagoran yan hamayyar 'yan siyasar kasar ta Gabon, Jean Ping, ya ce; Ba za su shiga cikin tattaunawar da shugaban kasa ya gayyace su ba.
Jean Ping wanda shi ne tsohon shugaban Kungiyar tarayyar Afirka ya zargi Ali Bongo shugaban kasar da yin magbudi a zaben da ya aka yi a 2016, tare da bayyana kansa a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai babbar kotun kundin tsarin mulki ta kasar ta yi watsi da zargin magudi a zaben tare da tabbatar da Bongo a matsayin shugaban kasa.
Bayan zaben na shekarar 2016 dai an sami hargitsi a cikin kasar ta Gabon wanda ya jawo asarar dukiya da rayuka.