Masar : An Bada Damar Sakin Husni Mubarak
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18488-masar_an_bada_damar_sakin_husni_mubarak
Bayan shudewar makonni biyu da kotun daukaka kara ta wanke tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak dangane da kisan masu zanga-zanga a lokacin juyin juya halin da ya hambarar da gwamnatinsa a shekara ta 2011, babban mai shigar da kara a kasar ya ce Mubarak zai iya tafiya gidansa.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Mar 13, 2017 15:58 UTC
  • Masar : An Bada Damar Sakin Husni Mubarak

Bayan shudewar makonni biyu da kotun daukaka kara ta wanke tsohon shugaban kasar Masar Husni Mubarak dangane da kisan masu zanga-zanga a lokacin juyin juya halin da ya hambarar da gwamnatinsa a shekara ta 2011, babban mai shigar da kara a kasar ya ce Mubarak zai iya tafiya gidansa.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, lauyan Husni Mubarak, mai suna Mubarak Farib Dib shi ne ya sanar da hakan a yau, inda ya ce babban mai shigar da kara ya ce da su Husni Mubarak zai iya tafiya gidansa, maimakon zama cikin gidan kaso bayan wanke shi daga laifin kisan jama'a.

Sai dai lauyan na Husni Mubarak ya kara da cewa, jami'an tsaro da ke gudanar da bincike kan dukiyoyin Mubarak ya mallaka sun sheda musu cewa, Husni Mubarak ba ya da hurumin fita daga kasar Masar a lokacin da ake bincike kan dukiyoyinsa da na iyalansa.