Kotu Ta yankewa Hamma Amadou Hukuncin daurin shekara guda a gidan Yari
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18496-kotu_ta_yankewa_hamma_amadou_hukuncin_daurin_shekara_guda_a_gidan_yari
Kotun daukaka kara A jamhuriyar Nijer ta yanke wa madugun 'yan adawa Hamma Amadou hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa safarar jarirai.
(last modified 2018-08-22T06:59:48+00:00 )
Mar 14, 2017 02:24 UTC
  • Kotu Ta yankewa Hamma Amadou Hukuncin daurin shekara guda a gidan Yari

Kotun daukaka kara A jamhuriyar Nijer ta yanke wa madugun 'yan adawa Hamma Amadou hukuncin daurin shekara daya a gidan yari bisa safarar jarirai.

Kotun ta yanke hukuncin ne duk kuwa  da cewa wanda ake zargin da kuma lauyansa sun fice  daga cikin  kotun.

An tuhumi tsohon shugaban majalisar dokokin kasar ta Nijer Malam Hamma Amadou tare da mai dakinsa da sayen jarirai  haihuwa daga Nigeria baya ga Hamma Amadou akwai wasu Mutane 20 da ake tuhuma da irin wannan Laifi.

Tsohon Shugaban Majalisar Dokokin tare da magoya bayan sa sun  sha musanta zargin inda suke kallonsa a matsayin wata kutunguilar siyasa.saidai Lauyoyinsa sun ce za su daukaka kara saboda a cewarsu an kauce wa ka’ida a yayin yanke wannan hukunci.