Karuwar Tauye Hakkin Bil'adama A kasar Sudan Ta Kudu
Mar 15, 2017 19:03 UTC
Majalisar Dinkin Duniya Ta yi Gargadi Akan Karuwar Tauye Hakkin Bil'adama A Kasar Sudan Ta Kudu Da Take Fama Da Yaki.
Shugabar hukumar kare hakkin bil'adama ta majalisar dinkin duniya, Yasmin Sooka, ta fada a yau laraba cewa; Abubuwa masu firgitarwa da tashin hankali suna faruwa, a kasar Sudan ta kudu,da su ka hada da yin fyade,kuma yin shirun kasashen duniya akai za iya kai wa ga kisan kiyashi.
Yasmin Sooka ta kara da cewa; Gwamnatin Sudan ta kudu da sojojinta, suna hulda da mutanen kasar ne a bisa kabilanci.
A gefe daya, ministan sharia na kasar ta Sudan ta kudu John Luk Jok ya yi watsi da rehoton na majalisar dinkin duniya, yana mai cewa babu gaskiya a cikinsa.
Tags