Nijar : An Kafa Kwamitin Da Zai Binciki Badakalar Kudaden Urenium
Majalisar dokoki a Jamhuriuya Nijar ta amunce da kafa wani kwamitinta da zai binciki badakalar nan ta wasu makuden kudaden Urenium da aka ce an karkata akalarsu daga Paris zuwa a wani banki dake birnin Dubai.
An dai kafa kwamitin ne mai mambobi goma bisa bukatar 'yan majalisa na bangaren adawa.
A watan Fabrairun da ya gabata ne wata jarida da ake bugawa a kasar mai suna le 'Le Courrier'' ta bankado labarin da aka ambato sunan ministan kudi na kasar Hassoumi Massaoudou a ciki.
A cewar jaridar, lamarin ya faru ne tun a shekara ta 2011, kuma bisa ga dukkan alamu kudaden da yawan su ya kai $ Milyan 319 an same su ne daga cinikin Uranium.
To sai dai Hassoumi Massaoudou daraktan fadar shugaban kasar a wancan lokaci, ya ce ba haka zance yake ba, wata haraka ce da aka samu kuma yaga cewa kasar zata samu riba ya sanya hannu a takardun.