Kimanin Mutane 20 Sun Mutu Sakamakon Faduwar Wata Bishiya A Kasar Ghana
Rahotanni daga kasar Ghana sun bayyana cewar kimanin mutane 20 sun mutu kana wasu da dama kuma sun sami raunuka a lokacin da wata katuwar bishiya ta faɗa musu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi a yammacin jiya a kasar.
Kafafen watsa labarai sun jiyo hukumar agajin gaggawa ta kasar tana cewa lamarin ya faru ne a a wani tudu da ruwa ke gangarowa a yankin Kintampo da ke yankin Brong-Ahafo da 'yan yawon shakatawa suke yawan kai ziyara wajen lokacin da ruwan sama ya barke da yayi sanadiyyar faduwar wata katuwar bishiya da ke wajen a kan mutanen da suke wajen.
Kakakin hukumar 'yan kwana-kwana na kasar Ghanan Anaglate ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa akasarin wadanda lamarin ya rutsa da su dalibai ne sai kuma wasu masu yawon bude ido, inda yace a nan take mutane 18 suka mutu kana wasu biyu kuma suka cika bayan an kai su asibiti.
Tuni dai gwamnatin Ghanan ta fitar da sakon ta'aziyya da juyayi ga iyalan wadanda hatsarin ya ritsa da su.