An fara taron kungiyar hadin kai Majalisu na kasashen Larabawa a Marocco
(last modified Tue, 21 Mar 2017 08:44:05 GMT )
Mar 21, 2017 08:44 UTC
  • An fara taron kungiyar hadin kai Majalisu na kasashen Larabawa a Marocco

Kungiyar Harin kan 'yan Majalisu na kasashen Larabawa sun fara taron su na 24 a Birnin Rabat fadar milkin kasar Marocco

Taron wanda zai dauki kwanaki biyu zai zabi sabon Shugaban kungiyar tare kuma da gabatar da sabin kudirin kungiyar na shekarar 2017.Rahotanni na cewa taron zai fi mayar da hankali kan halin da Duniyar Larabawa ke ciki a halin yanzu.

Har ila yau rahoton ya ce a gefen taron Kwamitocin kungiyar za tattauwa a tsakanin su.

A shekarar 1974 ne aka kafa wannan kungiya, da ta kumshi dukkanin Majalisun dokoki na kasashen Larabawa, manufar kafa wannan kungiya shi ne karfafa tattaunawa da tuntubar juna a tsakanin su , tare kuma  da daukan matakan bai daya a Majilisun Dokokin na kasashen Larabawa.