An Kame Shugaban Cibiyar Kare Hakkin Bil Adama Na Kasar Jibouti
(last modified Tue, 21 Mar 2017 18:54:45 GMT )
Mar 21, 2017 18:54 UTC
  • An Kame Shugaban Cibiyar Kare Hakkin Bil Adama Na Kasar Jibouti

Jami'an tsaron kasar Jibouti sun yi awon gaba da shugaban cibiyar kare hakkin bil adama ta kasar, wanda ya yi kaurin suna wajen sukar manufofin gwamnatin kasar dangane da dimukradiyya.

Kamfanin dillancin labaran AFP ya bayar da rahoton cewa, a yau babbar cibiyar kare masu fafutuka ta kasa da kasa ta fitar da wani bayani da ke cewa, jami'an tsaron gwamnatin Jibouti sun yi awon gaba da babban mai kare hakkokin bil adama na kasar Ali Awadu.

Tun kafin wannan lokacin dai Ali Awadu na fuskantar barazana daga bangaren gwamnatin kasar, tun bayan da ya fitar da wani jerin sunayen mutanen da aka kashe a kasar bisa dalilai na siyasa a cikin watan Disamban 2015.

Babbar cibiyar kare masu fafutuka ta kasa da kasa ta gargadi gwamnatin Jibouti a kan ta gaggauta sakin Ali Awadu, da ma duk wasu masu kare hakkin bil adama da ake tsare da su a kasar saboda dalilai na siyasa.