Masar : An Sallami Hosni Mubarak
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18796-masar_an_sallami_hosni_mubarak
Rahotanni daga Masar na cewa an sallami tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak daga gidan yari, shekara 6 bayan hambarar dashi daga mulki sakamakon boren 'yan kasar.
(last modified 2018-08-22T06:59:51+00:00 )
Mar 24, 2017 12:00 UTC
  • A farkon wannan wata ne kotun daukaka kara ta Masar ta bukaci da a saki Mista Mubarak
    A farkon wannan wata ne kotun daukaka kara ta Masar ta bukaci da a saki Mista Mubarak

Rahotanni daga Masar na cewa an sallami tsohon shugaban kasar Hosni Mubarak daga gidan yari, shekara 6 bayan hambarar dashi daga mulki sakamakon boren 'yan kasar.

Lauyen Mista Mubarak, Farid al-Deeb, ya bayyana a wannan Junma'a cewa an sallami shi, kuma tuni ya bar asibitin soji da ke kudancin birnin Alkahira inda ya tafi gidansa da ke garin Heliopolis da ke arewacin kasar.

Sakin tsohon shugaban kasar ya zo ma Misrawa da dama da mamaki, kana kuma ya fidda masu duk wani tunani na ganin boren da akayi a shekara 20011 ya tabbatar da mulkin demukuraddiya mai daurewa a kasar.

Ko baya ga Husni Mubarak, an wanke tsohon mataimakin cikin gidansa Habib al-Adly wanda keda hannu a kisa da muzgudanwa da kuma yin amfani da karfi mulki kan masu zanga-zanga a waccen lokacin na guguwar neman sauyi.

A farkon wannan wata da muke ciki wata kotun daukaka kara ta bukaci da a saki Mista Mubarak bayan ta wanke shi daga zargin kisan masu zanga-zanga a lokacin boren shekarar 2011.

Sakin wadanan jami'an na zuwa ne a daidai lokacinda matasan nan biyu da suka jagoranci boren waccen lokacin Alaa Abdel Fattah da Ahmed Douma ke garkame a gidan kurkuku.