Fataucin Makamai Da Miyagun Kwayoyi Na Dada Karuwa A Nijar
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i18918-fataucin_makamai_da_miyagun_kwayoyi_na_dada_karuwa_a_nijar
Rahotanni daga Nijar na cewa jami'an tsaron kasar a yankin Aderbisanat dake arewacin kasar sunyi nasara cafke makaman yaki kirar kalasknikov guda biyar da harsashai masu yawa ake shirin fataucinsu zuwa Diffa daga Zinder.
(last modified 2018-08-22T11:29:52+00:00 )
Mar 28, 2017 17:42 UTC
  • wasu makamai kirar AK 47 (hoto Air info) niger
    wasu makamai kirar AK 47 (hoto Air info) niger

Rahotanni daga Nijar na cewa jami'an tsaron kasar a yankin Aderbisanat dake arewacin kasar sunyi nasara cafke makaman yaki kirar kalasknikov guda biyar da harsashai masu yawa ake shirin fataucinsu zuwa Diffa daga Zinder.

Da yake tabbatar da hakan ga jaridar ''Air info'' a arewacin kasar, kantoman yankin Bukli Najim ya shaida cewa an gano makaman ne a lullube a cikin kayayakin da akayi lodinsu zuwa yankin na Diffa dake gabashin kasar.

Wannan kuma na zuwa ne a daidai lokacin da jami'an tsaron jandarman sukayi nasara gano kilo uku na kwaya da suma ake shiorin safararsu.

A cewar labarain wannan ba shi ne karaon farko ba da jami'an tsaron kasar ke yin nasara gano irin wadanan miyagun kayayakin, inda a kasa da wata guda ma anyi nasara gano dimbin kwalayen taramol da ake shiorin safarasu zuwa Libya.

Ko a kwanakin baya ma dai an gano dumbin harsashan bindiga da aka zuba a cikin bududuwa mai, lamarin dake nuna cewa safara makamai da miyagun kwayoyi na dada karuwa a wannan kasa a daidai lokacin da kasar ke fama da matsalar tsaro mai nasaba da mayakan jihadi dake fitowa daga Mali sai kuma 'yan ta'adda na Boko haram a yankin Diffa.